An fidda jar sanarwa a kan Kanar Gaddafi

Hukumar 'yan sanda ta duniya, ta fitar da jar sanarwa a kan Kanar Gaddafi da dansa Saiful Islam, da kuma tsohon jagoran jami'an tsaron kasar, Abdullah Al Sanussi.

'Yan sandan sun fitar da sanarwar ne bisa bukatar Kotun Munanan Laifuka ta Duniya, wadda can baya ta fitar da sammacin kama mutanen ukku, tare da tuhumarsu da aikata laifuka a kan bil adama.

Hakan dai na zuwa ne a lokacin da aka ambata ganin jerin gwanon motocin manyan magoya bayan Kanar Gaddafin sun shiga jumhuriyar Nijar, cikin su har da kwamandan dakarun gwamnatin Gaddafin a kudancin Libya.

Hukumomin Nijar dai sun ce an bar su ne sun shiga kasar bisa dalilan jin kai.