Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye da BBC Hausa: Ciwon sankaran mama

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Ciwon sankaran mama

Shirin na wannan makon zai duba matsalar ciwon sankaran mama wato ciwon dajin dake kama mama da kuma ko shin ya dace mai ciwon ta shayar, da kuma ko shin da gaske ne shayarwa na rage hadarin kamuwa da cutar.

Cibiyar Nazari akan ciwon sankara ta ce Cutar Cancer ko Sankara ko daji kamar yadda wasu suka santa dashi, cuta ce wadda wasu kwayoyin halitta wadanda basa aiki kamar yadda ya kamata, za su yi ta ninkawa babu adadi, yadda har zasu kai ga mamaye wasu sauran sassan jiki.

Hukumar lafiya ta Birtaniya NHS tace da wahala a iya gane musabbabin kowanne irin ciwon sankara wato daji ko cancer a turance, balle kuma a gangaro kan wanda ke kama nono, sai dai ta ce akwai wasu abubuwa da suke taimakawa wajen karuwar hadarin kamuwa da cutar.

Kamar yadda hukumar ta NHS ta yi bayani, shekaru ko gado, ko in wani a iyaye ko kakanni ya taba samun ciwon daji kowanne iri ne, ko kuma in macen ta taba gamuwa da wani nau'in ciwon dajin, ko ta sami wani kullutu a mamanta, ko mace me girman nono, ko kuma ga macen da ke fara al'ada da wuri, amma kuma shekarun kare al'adar su ja sosai, ko macen da take da teba, ko me matukar tsawo, ko wadda ke shan barasa, ko kuma in tururin wadansu na'urorin ya fiye shigar mace, duk na kara hadarin kamuwa da ciwon dajin mama.

Cibiyar bincike akan ciwon sankara ko daji ta Birtaniya ta bayyana alamomi na farko na ciwon sankarar dake kama mama da cewa shine kullutu a cikin nono. Sai dai ta ce sau tari kullutu tara cikin goma a mama baya kasancewa sankara.

Cibiyar binciken ta kara da cewa akwai wasu alamomi da ba lallai bane su ma a ce ciwon sankarar mama ne, amma daga zarar mace ta ga sauyi a fasalin mamanta, ko kuma zubar jini daga maman, ko ciwon mama, ko kuma kullutu ko kumburi a hammata to ta garzaya zuwa asibiti akan kari domin a bincika.

A wani bincike kuwa da sashen lafiya na BBC ya aiwatar, yace akwai yiwuwar mace daya a cikin mata tara a Birtaniya ta iya kamuwa da ciwon dajin mama a rayuwarta.

Binciken dai ya bayyana cewa a duk shekara akan gano masu dauke da cutar kimanin dubu arba'in da biyar.

Kuma shine babban musabbabin mutuwar mata 'yan tsakanin shekaru 34 zuwa 54 a kasar, wadda ita ce ke da mafi yawan wadanda ke mutuwa a saboda cutar a duk duniya kamar yadda binciken ya bayyana.

Shirin mu kenan na wannan makon. A yi sauraro lafiya.