Mutane tara suka hallaka a jihar Plato

Wasu rahotani daga jihar plato na cewa a jiya dare wasu mutane da ba'a san ko su wanene ba sun kai hari a kauyen tsohuwar Foron.

Kakakin gwamnatin jihar plato Mr Pam Ayuba ya shaidawa BBC cewa mutane tara aka kashe a jiya.

Lamarin na zuwa ne a dai dai lokacin da shafin wikileaks yace, manyan hukumomin tsaro na Nijeriya sun ja kunnen gwamnan jihar Plateau, Jonah Jang, da kada ya gudanar da zabukan kananan hukumomin da ya haddasa tashin hankalin da aka yi a watan Nuwambar shekara ta 2008 a jihar.

Amma shafin na Wikileaks ya ce gwamna Jang yayi buris da wannan jan hankali da aka yi masa.

Zaben dai ya haddasa asarar rayuka da dama a jihar ta Plateau wadda har yanzu take fama da rikicin addini da kabilanci.

To sai dai kuma gwamnan jihar ta Filato, Jonah Jang, ya bayyana cewa bayanan na Wikileaks zancen kawai ne kuma baya nadamar gudanar da zabukan na 2008, inda a karamar hukumar Jos ta arewa aka bayyana cewa wani dan uwan gwamnan ne ya lashe zaben kana tashin hankali ya barke.