Wani jirgin ruwa ya nitse a Tanzania

Hakkin mallakar hoto AP

Wani jirgin ruwan fasinja na Tanzania dauke da mutane kusan dari 6, ya nitse a cikin teku tsakanin tsibiran Zanzibar da Pemba, kuma.

An yi imanin cewa mutane da dama sun rasa rayikansu.

Ya zuwa yanzu dai, an gaano gawaki fiye da dari daya, kuma fasinjoji da dama sun bata.

Masu aikin ceto suna fuskantar matsala saboda jirgin ruwan, wanda ya kasance makare da jamaa fiye da kima, ya nItse ne a cikin dare.

Wani ma'aikacin ceto ya ce wadanda suka tsira da rayikansu sun hau kan katifu da firji da duk wani abu da ba zai nitse a ruwa ba.