Amurka na fuskantar barazanar ta'adanci

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Micheal Bloomberg magajin garin Newyork

Hukomomin Amurka sun ce sun samu bayanai masu karfi da ba'a tabbatar da su ba akan barazanar kai harin ta'adanci wanda kafafen yadda labarun kasar suka ce za'a kaiwa biranen New York ko Washington.

Bayanan sirrin da aka tattara daga harin da aka kaiwa Pakistan wanda yayi sanadiyar rasuwar Osama bin Laden na nuna cewa kungiyar Al qeada na kokarin gudanar da bikin ranar 11 ga watan Satumba ta hanya kaiwa Amurka hari.

Magajin garin New York, Micheal Bloomberg, ya tabbatar da cewa, akwai bayanai masu karfi dake nuna cewa ana barazanar kai hari a dai dai ranar zagayowar harin 11 ga watan satumba.

Gidan talibjin na ABC news ya ce akala mutane uku inda anyi amana daya daga cikinsu ba'amurke ne sun shigo cikin kasar a watan Augusta da anniyar kadamar da hari ta hanyar amfani da motoci.

A watan Mayun daya gabata Faisal Shazad wani dan kasar Amurka wanda ya halarci horaswa a wani sansani mayaka a Pakistan yayi yunkurin tada bam a dandalin times sqaure.

Tuni aka tsaurara matakan tsaro a birnin Newyork din yayinda ake shiryen shiryen gudanar da bikin.