Masar ta zartar da shirin ko ta kwana

Hakkin mallakar hoto reuters
Image caption Masu zanga zanga a ofishin jakadancin Israila

Gwamnatin Masar ta zartar da shirin ko ta kwana, bayan da masu zanga zanga suka yi amfani da karfi wurin shiga cikin ofishin jakadancin Israila a birnin Al-qahira.

An yi ta jin harbe harben bindigogi kuma mutane da dama sun samu raunuka.

Dakarun tsaro sun yi amfani da hayaki me sa hawaye domin tarwatsa daruruwan mutanenda suka lalata wani bango dake samar da kariya ga ofishin jakadancin.

Masu zanga zangar dai sun fusata ne bayanda sojojin Israila suka hallaka dakarun Misra guda biyar a watan jiya.

Shaidun da suka gani da idanunsu sun ce an zubar da takardun da aka rubuta da harshen yahudanci daga winduna a kan daruruwanan jama'ar dake kasa wadanda ke shewa.