An sake samun tashin hankali a Jos

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jamian tsaro a Jos

Rahotani daga jihar Plato na cewa wasu mutane da ba'a san ko su wanene ba sun kai wani sabon hari a kauyen Vwang dake karamar hukumar jos ta kudu.

Kakakin gwamnatin jihar Mr Pam Ayuba ya tabbatarwa bbc da kai harin a jiya da dare inda ya ce an samu asarar rayuka da dama.

Lamarin na faruwa ne a dai dai lokacin da wata takaddama ta kunno kai tsakanin gwamnan jihar Filato Jonah Jang da tsohon janar din sojan Nijeriya, Jeremiah Useni, dangane da tashe-tashen hankula da ake fama da su a jihar ta Filato wadanda suka ki ci suka ki cinyewa.

Janar Jeremiah Useni dai ya zargi gwamnan da rashin jin shawarwari na yadda za a kawo karshen tashe-tashen hankulan, da rashin kulawa da halin da jihar ke ciki sannan ya ce wajibi ne gwamnatin Nijeriya ta sani cewa barin batun magance rikicin a hannun gwamnan zai kara jefa rayukan mutane a jihar cikin hadari.

Sai dai bangaren gwamnan sun maida martani inda suka ce ai ba dole ba ne a yi aiki da shawara idan aka bayar, kuma gwamnatin jihar na iya kokarinta wajen magance tashe-tashen hankulan.