Yan tawaye sun shiga garin Bani Walid

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani dan tawaye a garin Bani Walid

Dakarun dake adawa da kanar Muammar Gaddafi, sun shiga Bani Walid, daya daga cikin garuruwa na karshe da suka rage a hannun sojojin dake biyayya ga kanar Gaddafin, kuma an yi dauki ba dadi a wajen birnin.

Ya ragewa dakarun dake adawa da Gaddafi kilomita biyu ne su shiga birnin, bayanda suka kutsa cikin gaggawa da rana.

Wakilin gwamnatin rikon kwaryar yan tawayen a Birtaniya Guma el Gamaty ya ce yan sa'oi kalilan ya rage masu su kwace garin.

Mayakan sun ce basu da wani zabi illa su kusa kai cikin garin bayan da aka kai musu hari da rokoki.

Yunkurin da aka yi domin shawo kan daruruwan magoyan bayan kanar Gaaddafi su mika garin ba tare da fada ba ya citura a farkon makon da muke ciki.