A yau sakatare janarar na kungiyar larabawa zai isa Syria

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Masu zanga zanga a Syria

Sakatare janar na kungiyar hadin kan larabawa na gab da ci gaba da ziyararsa da aka jingine zuwa kasar Syria a yau asabar, kwana guda bayanda aka samu karin masu zanga zangar adawa da gwamnatin kasar.

Ana sa ran Nabil al-Arabi zai gabatar da sharwarwarin kungiyar hadin kan Larabawan na irin sauye sauyen siyasa da ya kamata gwamnatin Syriar ta aiwatar.

A jiya Juma'a ne dai, masu zanga zangar suka yi kira ga kasashen duniya da su basu kariya daga irin hare harenda jamian tsaron gwamnati ke kaiwa akansu.

Rahotanni dai na nuna cewa an samu karin mutanenda suka rasu.