Bama-bamai sun fashe a jihar Filato

Image caption Gwamnan Filato, Jonah Jang

A Najeriya, hukumomi a jihar Filato sun ce wadansu bama-bamai guda biyu sun tashi a babban birnin jihar, Jos.

Mutanen da suka ji karar tashin bama-baman sun shaidawa BBC cewa sun firgita sosai, inda kowa ya yi ta kansa. Kakakin rundunar tabbatar da tsaro da ke jihar, Kyaftin Charlse Okocha, ya shaidawa wakilinmu, Is'haq Khalid, cewa bama-baman sun tashi ne a unguwar West of Mine da ke birnin.

Ya ce babu wanda ya rasa ransa sakamakon tashin bama-baman.

Sai dai ya ce a ranar Litinin da safe ne za su yiwa manema labarai cikakken bayani game da tashin bama-baman.