Bikin tunawa da harin September 11

Image caption Barak Obama

A yau Lahadi ne Amurka ke cika shekaru goma tun bayan hare-haren da aka kaiwa kasar na ranar sha daya ga watan Satumbar shekarar 2001.

An baiwa jama'a damar gudanar da addu'o'i ga wadanda suka mutu a hare-haren.

An shirya gudanar da nune-nune na kayyaki da kuma kade-kade, inda kuma jami'an 'yan sanda da 'yan kwana-kwana za su yi jerin gwano zuwa cibiyar kasuwanci ta duniya da ke New York, inda aka fara kai hare-haren.

A jawabinsa na mako-mako, shugaban Amurka, Barack Obama ya ce yanzu lokaci ne na gina kasa, inda ya ce ana daukar dukkan matakan da suka wajaba don kare rayukar jama'ar kasar.

Shugaba Obama da tsohon Shugaba, George Bush za su yi jawabi a karshen bikin tunawa da zagayowar ranar.