Abdul Jalil ya nemi hadin kan 'yantawayen Libya

Shugaban majalisar wucin gadin 'yan tawayen Libya, NTC, Mustafa Abdul Jalil, ya yi gargadin cewa har yanzu Kanar Gaddafi yana da makudan kudaden da zai iya sayen sojan haya, don cigaba da yaki.

Mr Abdul- Jalil ya ce akwai bukatar hadin kai daga dukannin 'yan tawayen Libya, domin 'yanto garuruwan da suka rage a hannun magoya bayan Kanar Gaddafin, wadanda suka hada da Sirte da Bani Walid da kuma Sabha.

Shugaban majalisar ta NTC, yana magana ne a ranar farko da ya fara aiki a Tripoli, inda ya isa a jiya dad dare, bayan da ya taso daga Benghazi.