Shugaban Masar zai bayar da shaida

Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Mista Tantawi

Shugaban mulkin sojin Masar, Mohammed Hussein Tantawi, zai bayar da shaida a shari'ar da ake yiwa tsohon shugaban kasar, Hosni Mubarak.

Mista Mubarak, wanda ke da shekaru tamanin da uku a duniya, na fuskantar hukuncin kisa idan aka same shi da laifi na bayar da umarnin kashe mutanen da suka gudanar da zanga-zanga a kasar a farkon wannan shekarar.

Zanga-zangar dai ta yi sanadiyar kifar da gwamnatinsa.

Shaidar da Mista Tantawi zai bayar za ta yi tasiri a shari'ar.

Hakan na zuwa a dai-dai lokacin da 'yan kasar suka kai hari a ofishin jakadancin Israela da ke Masar.