Saadi Gaddafi ya na kasar Nijar

Image caption Shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun ce Saadi Gaddafi, daya daga cikin 'ya'yan Kanar Mu'ammar Gaddafi, da mukarrabansa sun shiga kasar.

Ministan shari'a, kuma kakakin gwamnatin Nijar din, Malam Maru Amadou, shi ne ya tabbatar da hakan a cikin wata hira da BBC a ranar Lahadi.

Ya ce jami'an tsaron Nijar ne suka gano Saadi Gaddafin, da wasu mutanen su takwas, kuma yanzu haka suna yankin Agades, a kan hanyarsu ta zuwa Yamai, babban birnin kasar.

A cikin 'yan kwanakin da suka wuce, mukarraban Kanar Gaddafi da dama sun shiga jamhuriyar ta Nijar.