Hatsarin nukiliya a Faransa

Tashar nukiliya ta Marcoule a Faransa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tashar nukiliya ta Marcoule a Faransa

Mutum daya ne ya mutu a yayinda wasu hudu suka jikkata a lokacin da wani abu ya fashe a wata tashar sarrafa makamashin nukiliya dake Marcoule na kusa da birnin Nimes a kudancin Faransa.

Hukumar kiyaye hadarin makamashin nukiliya a Faransa ta ce ba'a samu yoyon tururin nukiliya ba a tashar, amma dai an tsaurara matakan tsaron a wurin.

Da yake magana da manema labarai a birnin Vienna a Austria, Sakatare Janar din Hukumar kula da makamashi nukiliya ta duniya, IAEA, Yukiya Amano ya ce yana tattaunawa da mahukanta a Faransa domin tantance abun da ya faru.