Bututun mai ya kashe mutane da dama a Kenya

Bututun mai ya kashe mutane da dama a Kenya
Image caption Jama'a da dama ne lamarin ya ritsa da su

'Yan sanda sun ce akalla mutane 120 ne suka mutu bayan da wata wuta ta tashi sakamakon fashewar wani bututun mai a Nairobi babban birnin kasar Kenya.

Lamarin ya afku ne a yankin masana'antu da ke Lunga Lunga, kuma masu aikin kashe gobara na kokarin kawar da hayakin da ke barazanar mamaye wani gari da ke kusa da wurin.

Bututun man ya ratsa ne ta wani yanki da ke da yawan jama'a tsakanin tsakiyar birnin Nairobi da kuma filin saukar jiragen sama.

Mahukunta sun ce an garzaya da mutane fiye da 80 da hadarin ya ritsa da su zuwa asibiti.

Wani ma'aikacin agaji ya ce yawancin wadanda lamarin ya ritsa da su sun kone kurmus.

Babu masaniya kan abin da ya haddasa fashewar.

Mazauna wurin sun ce da farko da bututun ya fashe, jama'a sun garzaya domin dibar mai daga wurin.

"Daga nan ne kuma sai muka ji kara, da hayaki da kuma wuta," wani mazaunin yankin Joseph Mwego ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Abaya ma jama'a sun sha mutuwa a lokacin da suke kokarin dibar man da ke zuba: Fiye da mutane 100 ne suka mutu a yankin Molo, a shekara ta 2009 bayan da wuta ta tashi daga wata motar daukar mai.