An zafafa bukatar neman 'yancin Palasdinu

Mahmud Abbas Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas ya na ganawa da jagoran Hamas Khaleed Mishal

Kungiyar fafutukar 'yancin Plasdinu (PLO) za ta gabatar da bukatar neman amincewa da yankin ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya duk da adawar da Amurka ke nunawa.

Sanarwar ta fito ne daga bakin Mohammed Shtayyeh, wani babban jami'i a jam'iyyar Fatah a wani taron manema labarai a birnin Ramallah.

Sanarwar ta sa ta kawo karshen rade-radin da ake yi kan matakin siyasar da Kungiyar ta PLO za ta dauka.

"Za mu tunkari Majalisar Dinkin Duniya, za mu tunkari Kwamitin Sulhu" a cewar Shtayyeh. "Za mu nemi a bamu cikakken 'yancin kai karkashin iyakokin shekarar 1967.

Mahmoud Abbas, shugaban Palasdinawa zai gabatar da jawabi ranar Juma'a a Ramallah inda zai yi cikakken bayani kan shirin.

Amincewa da Palasdinu a matsayin kasa zai ba ta damar kada kuri'a a Majalisar Dinkin Duniya da shiga kotun hukunta laifukan yaki ta duniya da kuma sauran hukumomin duniya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zangar neman 'yancin Palasdinu a birnin Ramallah

Matsalar da Kungiyar PLO din za ta fuskanta wajen samun kashi biyu bisa uku a babban zauren Majalisar Dinkin Duniyar bashi da yawa; tuni fiye da kasashe 120 su ka yi alkawarin mara wa yunkurin na ta baya, kamar dai yadda Saeb Erakat, babban mai shiga tsakani na Palasdinu ya ce.

Sai dai tuni Fadar gwamnatin Amurka White House da wasu Jami'an Amurkan su ka ce za su yi amfani da ikon kada kuri'ar da suke da shi wajen dakile yunkurin Palasdinu, tun da ba za ta taba cimma haka ba sai da amincewar kwamitin sulhu.

Duk da haka wasu Palasdinawa na kira ga hukumominsu da su share Amurka, su nufi babban taron Majalisar kai tsaye.

Ba tabbas kan mataki na gaba

Shtayyeh ya bayyana cewa, ko da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wannan kuduri, ba zai sauya rayuwar Palasdinawa ta yau da kullum nan take ba.

"Abubuwan dake kasa ba za su sauya ba," a cewarsa. "Banbancin zai faru ne kawai a matakin siyasa. Palasdinawa za su shiga cikin Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya....... Sannan kuma ba za a sake daukar yankunan Palasdinu da cewa 'yankin da ake takaddama akai ba' sai dai a ce yankin da aka mamaye."

Shtayyeh yace Kungiyar PLO ba ta yanke hukunci kan martanin da za ta mayar akan adawar da Amurka ke nuna mata ba.

Za ta iya karar babban zauren Majalisar Dinkin Duniya kan daukaka matsayin ta, ko kuma ta sake komawa kwamitin Sulhu domin tursasa wani ikon kada kuri'ar.

Sanarwar dai na nuni da cewa Kungiyar PLO ta shirya ci gaba da wannan yunkuri, duk kuwa da adawar da Amurka da wasu kasashen za su kawo domin dakile ta.

Karfafa gwiwa

Fira ministan Turkiyya, Recep Tayyip Erdowan, ya shaida wa kasashen Larabawa cewa tabbatar da kasar Palasdinu wajibi ne ba wai zabi ba.

A jawabin da ya yi a wajen taron shugabannin kasashen Larabawa da ake yi a birnin Alkahira, Mr Erdowan ya sake yin kakkausar suka kan gwamnatin Isra'ila, inda ya ce ita ce sanadin hana zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, ta kuma datse jama'arta a waje guda.

Taron kungiyar kasashen Larabawan na tattaunawa kan yadda za'a taimakawa Palasdinawa su samu 'yantacciyar kasarsu idan an kai batun gaban Majalisar Dinkin Duniya nan gaba a cikin wannan watan.

Wadannan kalamai na zuwa ne a daidai lokacin da kasashe daban-daban ke kara bayyana goyon bayansu ga matakin Hukumomin Palasdinu.