Hukumar SSS ta gurfanar da mutane 8 a gaban Kotu

Wadanda ake zargin yan Boko Haram ne Hakkin mallakar hoto AP

Hukumar leken asirin Najeriya ta SSS, ta gurfanar da wasu mutane takwas da ta ce 'yan Boko Haram ne, a gaban wata kotun Majistare da ke Abuja.

Hukumar leken asirin ta Nigeria tana zargin mutanen ne da kai hare haren bomb a Abuja, da kuma a karamar hukumar Suleja da ke jihar Naija, mai makwabtaka da Abujar.

Kimanin mutane ashirin da hudu ne suka mutu a hare-haren da aka kai tsakanin watan Maris da Agusta na bana.

Daya daga cikin mutanen da aka gurfanar a gaban kotun ya amsa cewar a can baya ya taba zama dan kungiyar Boko Haram.

Ahmed Hassan Ezimakor, ya ce bashi da hannu a harin, to amma ya taimaka wajen samun boma-boman da aka kai hare haren da su.

Dukan mutanen da ake tuhumar dai sun musanta zargin da ake yi musu.