Hukumar tantance masu wa'azi a Katsina

Image caption Masallaci

A Najeriya, gwamnatin jihar Katsina ta kafa wata doka wacce za ta sa ido akan duk wadansu harkoki na addinin Islama.

Wannan doka da gwamnan jihar, Barrister Ibrahim Shehu Shema ya sanyawa hannu ta haramta yin wa'azi da limanci, da jagorantar duk wasu harkoki na yada addini ba tare da izini ba.

A karkashin dokar, an kafa wata hukuma da ake kira "Hukumar kula da harkokin ilmin addini da wa'azi da sauran al'amurra", kuma wannan hukumar ce za ta rinka bayar da lasisi ga masu wa'azin da limamai.

Sai dai wani malami a jihar, Sheikh Yakubu Yahya, ya ce kafa irin wannan dokar ba ya daga cikin hurumin gwamnati tun da dai ta ce babu ruwanta da batun addini.

Ya kara da cewa ba kowanne malami ne zai yi biyayya ga dokar ba.

Amma Gwamna Shema ya ce dokar ba sabuwa ba ce, illa dai suna so ne su jaddada ta ne kawai.