Amurka ta yi wa Libya alkawarin samun kwakkwaran goyon baya

Jeffrey Feltman Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jeffrey Feltman, Wakilin Amurka na musamman

Babban jami'in gwamnatin Amurka na farko da ya fara kai ziyara Tripoli tun bayan da aka hambarar da Kanar Gaddafi, yayiwa mahukuntan gwamnatin rikon kwaryar Libya alkawarin samun dukkanin goyan bayan da ya dace wajen sake gina kasar bisa tafarkin demokuradiyya.

Jami'in, Jeffrey Feltman ya ce, Amurka a kodayaushe za ta amince da Libya a matsayin kasa mai yancin kanta, kuma duk wata alakarsu za ta kasance ta yadda mahukuntan Libyan ke bukata.

Ya ce, wannan wata nasarace ga jama'ar Libya, kuma su kadai ne zasu iya yanke shawarar yadda suke san makomarsu ta kasance.

Mr Feltman ya ce, Amurka bata shiga Libya ba domin farautar kanal Gaddafi ba saboda baya cikin aikin da ya kai kungiyar NATO kasar na kare fararan hula.