Za a yi taro game da kasashen Turai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tutocin kasashen Tarayyar Turai

A yau Laraba ce shugabannin kasashen Jamus, da Faransa, da Girka za su tattauna game da matsalar tabarbarewar tattalin arzikin da ke karuwa a kasashen Tarayyar Turai.

Za su yi tattaunawar ce ganin irin mawuyacin halin da kasuwannin hada-hadar hannayen jarin kasashen ke ciki, da kuma fargabar da ake yi cewa mai yiwuwa kasar Girka ta kasa biyan basussukan da ake bin ta.

Ana sa ran jami'an Asusun Ba da Lamuni na Duniya, da na Tarayyar Turai, da kuma jami'an Babban Bankin Tarayyar Turai za su sake komawa kasar Girka nan ba da dadewa ba, don sake yin nazari akan ko kasar ta cancanci samun wani sabon tallafi.

Dole ne a baiwa kasar Girka sabon tallafin kudi idan tana bukatar hakan, idan ba haka ba ta tsiyace.