Cameron da Sarkozy sun isa Libya

David Cameron da Sarkozy
Image caption Su ne shugabannin Yamma na farko da suka je kasar ta Libya

Fira ministan Burtaniya David Cameron da shugaban Faransa Nicolas Sarkozy na kasar Libya, a karon farko tun bayan da aka hambarar da gwamnatin Kanal Gaddafi.

Kasashensu na kan gaba a matakan da Nato ke dauka kan kasar ta Libya.

Za su gana da shugabannin gwamnatin rikon kwaryar kasar ta NTC a Tripoli, kafin su tashi zuwa Benghazi, inda ake saran za su yi jawabi a dandalin 'yanci na birnin.

Shugaban NTC Mustafa Abdul Jalil ya yi musu alkawarin cewa "za su samu cikakken tsaro".

A ranar Laraba, ya nemi a taimaka musu da makamai domin samun damar kwace sauran garuruwan da har yanzu ke hannun magoya bayan Kanal Gaddafi.

Ya shaida wa BBC cewa har yanzu tsohon shugaban yana nan a kudancin kasar inda ya ke yunkurin ramuwar gayya.

Wani rubutaccen sako da aka ce ya fito ne daga Gaddafi ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta dakatar da "muggan laifukan" da ake aikatawa a mahaifarsa ta Sirte.

Gaddafi wanda ya mulki kasar na tsawon shekaru 42, a baya ya ce ba inda za shi har sai ya mutu a Libya.

Nato na kai hare-hare a kasar ta sama karkashin kuduran Majalisar Dinkin Duniya guda biyu domin kare fararen hula, kamar yadda suka ce.

A nata bangaren, Amurka ta ce ta samu kwarin gwiwa ne daga irin ikon da Majalisar NTC ke kara samu a yankunan kasar daban-daban.