Sarkozy zai kai ziyara Libya

Shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy

Rahotanni sunce Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy zai kai ziyara birnin Tripoli a yau, domin gabatar da wani jawabi a dandalin Liberty.

Haka kuma shugaban daga bisani zai ziyarci birnin Benghazi a Libya.

Kafar yada labaran Faransan ta ruwaito cewar shugaban zai samu rakiyar Henri Bernard Levy mai ilimin falsafa wanda ake masa kallon wanda ya baiwa Shugaba Sarkozy shawarar daukar matakin soji a kasar Libya.

A waje daya kuma Burtaniya ta rarraba wani daftarin shawarwari ga kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya da zai yi sassauci kan takunkumin da majalisar dinkin duniyar ta kakabawa Libya.