Cameron da Sarkozy sun ziyarci Libiya

Cameron da Sarkozy a Libiya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Cameron da Sarkozy a Libiya

Kasahen Birtaniya da Faransa sun shaidawa Libya cewa har yanzu da sauran aiki a yunkurin neman zaman lafiya a kasar.

A wani taron manema labarai a Tripoli, Firayim Ministan Birtaniya David Cameroun ya ce kungiyar tsaro ta NATO za ta ci gaba da kai hare-hare, har sai an ga bayan sauran 'yan gani- kashenin Gadaddafi da suka rage.

Shugaban Faransa Nicholas Sarkozy yayi kashedin cewa har yanzu da sauran hadari.

Shugabannin biyu sun kuma ziyarci Bangazi inda aka yi masu kyakkyawar tarba

Mr. Sarkozy da Firayim Minista Cameron sune shugabannin kasashen waje na farko da suka ziyarci Libya tun bayan hambaradda Kanar Gaddafi.

A halin da ake ciki kuma, majalisar wucin gadin Libya ta ce dakarun da ke adawa da Gaddafi suna dabda da Sirte Mahaifar Gaddafi.

Wani kakaakin majalisar ya shaidawa BBC cewa dakarun sun wuce bakin dagar da dakarun Gaddafi suka shata ta yammaci, kamar kilomita 8 daga tsakiyar garin.

Sai dai kakaakin yace sun fuskanci turjiya, abunda ya sa wasunsu ja da baya da kamar kilomita 2 don yiwa 'yan uwansu da suka ji ciwo a artabun magani.

Kawo yanzu dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da hakan.