Cameron da Sarkozy a Libiya

Cameron da Sarkozy a Libiya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Cameron da Sarkozy a Libiya

Praministan Birtaniya, David Cameron, da shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy, na wata ziyara a kasar Libya.

Su ne shugabannin kasashen waje na farko da suka ziyarci birnin Turabulus ko Tripoli, tun bayan da 'yan tawaye suka karbe iko da shi, suka kuma kori Kanar Gaddafi a watan jiya.

Sun shaidawa sabbin mahukuntan Libiyar cewa, har yanzu da sauran aiki, a yunkurin neman zaman lafiya da akeyi a kasar.

A wani taron manema labarai a Tripoli, Praministan Birtaniya ya ce, kungiyar tsaron NATO zata cigaba da kai hare-hare, har sai an ga bayan sauran 'yan gani- kashenin Gaddafi da suka rage.

Shi kuma shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, ya ja kunnen 'yan kasar akan daukar fansa, tare da yin alkawarin cewa za'a hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Mr. Sarkozy ya kuma yi watsi da duk wani zargin cewa sun je Libiyar ne saboda giwa ta fadi.