Kwamiti ya maida martani kan rahoton rikicin Jos

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jam'an tsaro a garin jos mai fama da rikici

Daya daga cikin shugabannin kwamitin da shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan ya kafa domin ya binciki rikicin jihar Filato karkashin jagorancin Cif Solomon Lar, ya nuna rashin jin dadinsa na neman aiwatar da rahoton kwamitin a yanzu ba. Tun a bara ne dai kwamitin ya mika rahotonsa ga shugaban Najeriya, amma sai a wannan makon shugaban ya nuna cewa zai hanzarta aiki da rahoton, dama sauran rahotonnin kwamitocin binicike na tarrayya kan rikicin jihar Filato. Ambasada Yahaya Kwande, shine shugaba na biyu na kwamitin ya ce idan aka aiwatar da rahoton kamar yadda suka bada shawara, to kuwa rikici a jihar Filaton zai zama tarihi cikin dan kankanin lokaci.