Dakarun Libya na sa kaimin kama Sirte

Dakarun da ke adawa da Kanar Gaddafi sun kara bude wuta a kan Bani Walid da Sirte, garurwa biyu da suka rage da ke karkashin ikon magaoya bayan Gaddafi.

Amma kuma suna fuskantar matukar turjiya.

Wani kamandan 'yan tawayen ya ce, a shirye suke ayi ta kare.

A halin da ake ciki kuma, babban taron majalisar dinkin duniya ya bayar da kujerar wakilcin kasar ta Libya ga majalisar wucin gadin kasar .

A kuri'ar da aka kada, kasashe dari da goma sha hudu ne suka amince da kudirin, kuma 17 suka ki.

Wasu kasashe a nahiyar kudancin Amurka ba su goyi bayan kudirin ba, yayinda wasu kasashen Afrika suka so a jinkirta shawarar.