Sojan Nijar sun kara da 'yan al Qaeda'

Taswirar Nijar Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Taswirar Nijar

Ma'aikatar tsaron Nijar ta ce, an yi artabu har sau biyu a cikin wannan watan, yankin Agadez na arewacin kasar, tsakanin sojojin gwamnati da kungiyar al Qaeda a yankin Maghreb, da kuma wasu da ake zargin masu fataucin miyagun kwayoyi ne.

Artabu na baya bayan nan shi ne wanda ya faru a jiya.

Jami'an tsaro 2 suka rasa rayukansu yayin da wasu 3 suka sami munanan raunuka.

Ma'aikatar tsaron Nijar din ta ce 'yan ta'adda 6 ne suka hallaka a lokacin fadan, kuma jami'an tsaro sun kwato motoci da makamai da dama.

Haka ma an kwato wasu matasa fiye da 50, wadanda aka ce kungiyar ta al Qaeda ta dauka aiki ba tare da son ransu ba.