'Yan adawan Syria sun kafa kungiya daya

Zanga-zanga a kasar Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zanga-zanga a kasar Syria

'Yan adawa a kasar Syria sun ce sun cimma kafa majalisar kasa da zata samu wakilcin dukkannin bangarorin dake adawa da gwamnatin shugaba Bashar al-Aasad.

Sun bada wannan sanarwar ce a Istanbul, watanni shida bayan soma zanga-zanga a kasar ta Syria.

Majalisar ta kunshi mutane 140 mafiyawa daga cikinsu mazauna kasar ta Syria, sai dai akwai yiwuwar ta fuskanci manyan kalubale saboda banbance-banbance dake tsakanin mambobinta.