An sassauta takunkumi akan Libya

Mayakan 'yan tawayen Libya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mayakan 'yan tawayen Libya

Kamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya sassauta takunkumin da ya kakabawa Libya tare da kafa kungiya ta majalisar da zata taimakawa majalisar rikon kwaryar kasar Libyan da shawarwari.

Sassaucin dai ya hada da sake kadarorin wasu kamfanonin man Libya guda biyu da kawo karshen hana zirga-zirgan jiragen 'yan kasuwa a kasar.

Hakan ya zo ne watanni shida bayan majalisar ta dauki matakin soji don kare fararen hula a yakin da 'yan tawaye da dakarun gwamnatin Gaddafi ke fafatawa.

Majalisar dinkin duniya dai ta amince ta baiwa 'yan tawayen kujerar Libya a majalisar.