Nijar ba za ta mika jami'an Ghaddafi ba

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar Libya, Abduljalil Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban gwamnatin rikon kwaryar Libya, Mustapha Abduljalil

Ministan shari'a kuma kakakin gwamnatin Nijar, Malam Maru Amadu, ya jaddada cewa Nijar ba za ta mika jami'an gwamnatin Gaddafi ga wata hukuma ko kasa inda ba za'a yi musu adalci ba, ko ma a hallaka su.

Haka kuma ya musanta labarin dake cewa kasar Faransa na son ta sa baki don Nijar ta mika jami'an ga hukumar wucin gadin kasar Libya wato NTC.

Kakakin gwamnatin ya kuma ce kasar ba za ta yarda jami'an gwamnatin Ghaddafin dake zaman mafaka a Nijar su yi zagon kasa ko makarkashiya ga gwamnatin rikon kwarya ta 'yan tawayen Libya daga Nijar ba.