An gabatar da shawarar lokacin fara zabe a Masar

Fiel Marshal Mohammed Tantawi, shugaban majalisar mulkin sojan Masar Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Field Marshal Mohammed Tantawi, shugaban majalisar mulkin sojan Masar

An bada shawarar lokacin gudanar da zaben majalisar dokoki a kasar Masar, bayan tarzomar da aka gudanar a wata Fabrairu da ta kifar da gwamnatin Shugaba Hosni Mubarak, da ya kwashe shekaru talatin yana mulki.

Wakilin BBC ya ce karkashin jadawali da aka bada shawarar aiki da shi, za a gudanar da zaben farko ne ranar 21 ga watan Nuwamba.

Sai dai babu wani bayani da aka bayar kan ranar zaben shugaban kasa.

Wakilin na BBC a Alkahiran ya ce mai yuwuwa nan da mako guda majalisar soja, mai mulkin kasar za ta fitar da shawarar karshe kan batun.

Ya ce yan adawa na fatan a wannan karon, za a gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci, bayan shekara da shekaru ana tafka magudi.