Wa'adin 'yan bindiga a Niger Delta ya kare

Sojan kungiyar dakarun tsaro na hadin guiwa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sojan kungiyar dakarun tsaro na hadin guiwa a yankin Nger Delta, Najeriya

A Najeriya a yau ne wa'adin da aka dibawa 'yan bindiga a yankin Niger Delta mai arzikin mai na su mika makamansu ke karewa.

Kungiyar dakarun tsaro ta hadin gwiwa ce ta dibawa 'yan bindigar wannan wa'adi, bayan wasu hare- hare da 'yan kungiyar Boko haram suka kaddamar.

Mai magana da yawun kungiyar tsaron, Timothy Antiga yace bayan cikar wa'adin, za'a kama duk wanda aka samu da wani makami.

Rundunar sojin Najeriya dai ta kara tsaurara matakan tsaro akan kayayyakin kamfanonin mai a yankin na Niger Delta.