An yi girgizar kasa a India

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Irin barnar da girgizar kasa ta yi a India

Wata mummunar girgizar kasa mai karfin maki shida da digo tara ta afku a yankin Himalayas na kasar India inda akalla mutane ashirin da shida suka mutu.

Girgizar kasar ta fi kamari ne a jihar Sikkim da ke yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Jami'an 'yan sanda da 'yan jaridu sun ce ruwan saman da ake tafkawa da kuma zabtarewar laka na kawo cikas a kokarin da ake yi na ayyukan ceto.

An kuma ba da rahotannin da ke cewa wasu mutane sun mutu a yankunan Bihar, da Tibet, da Nepal na kasar.