Nijar ta nemi taimako kan harkar tsaro

Shugaban Kasar Nijar, Alhaji Mahamadou Issoufou, ya yi kira ga kasashen duniya da su taimakawa kasar wajen horar da Jami'an tsaronta, da kuma kayan aiki na zamani domin shawo kan matsalar ta'addancin da kasar ta Nijar ke fama da ita a yankin arewaci.

Shugaban na Nijar ya yi wannan kira ne yau a wajen bude taron kungiyar kasuwanci ta duniya a birnin Geneva.

Shugaban ya ce hakan ya zama wajibi a yunkurin da ake yi na tunkarar tabarbarewar tsaro a yankin sahel sakamakon rikicin Libiya.

Shugaban na Nijar ya ce wannan al'amari zai iya yin tasiri ga harkokin kasuwanci, da shige-da -ficen jama'a, a yankin na Sahel.