Martani kan kiran tallafawa Nijar game da batun tsaro

Shugaban Nijar, Alhaji Issoufou Mahamadou
Image caption Shugaban Nijar, Alhaji Issoufou Mahamadou

A jamhuriyar nijar, jama'a da kungiyoyi na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu game da furucin da shugaban kasar, Alhaji Isufu Mahamadu ya yi , na neman kasashen duniya su taimakawa kasar da kayan aiki tare da horar da jami'an tsaronta domin tunkarar matsalar tsaro da ya ce kasar na fuskanta.

Yanzu haka kawancen adawa na ARN na ganin kamata ya yi gwamnatin ta nemi shawara a cikin gida kafin ta fita waje, sannan ta yi kokarin hada kan jami'an tsaron kasar da ya ce na fama da matsaloli a tsakaninsu yau da 'yan watanni.

Sakataren yada labarai na jam'iyyar MNSD-Nasara wadda ke jagorancin kawancen na ARN, Malam Issoufou Tamboura ya ce kiran da shugaba Issoufou Mahamadou ya yi, zai iya sa kasashen Yammacin duniya su nemi kafa sansanoninsu a cikin Nijar, kamar yadda ta faru a kasashen Cadi da Gabon da Jumhuriyar Afrita Ta Tsakiya da kuma Cote D'Ivoire, abun da ya janyo rikice-rikice a wadannan kasashe.