Ganawa tsakanin gwamnati da tsofaffin 'yan tawayen Nijar

Image caption Shugaban Nijar, Mahamadou Isoufou

A Jamhuriyar Nijar, an yi wata ganawa tsakanin hukumar da ke kula da wanzar da zaman lafiya da kuma tsofaffin 'yan tawayen kasar.

Hukumomin kasar dai sun shirya ganawar ce da nufin tattauna matsalolin da tsofaffin 'yan tawayen ke fama da su tun bayan da suka ajiye makamai, kana su lalubo hanyoyin warware matsalolin.

Kanar Abu Tarka shi ne shugaban hukumar koli mai maido da zaman lafiya a kasar, ya shaidawa BBC cewa sun bukaci tsofaffin 'yan tawayen su ba su hadin kai wajen gudanar da ayyukan ci gaban kasar.

Ya ce gwamnati ta gudanar da ayyuakan da za su bunkasa rayuwar tsofaffin 'yan tawayen, kuma ba za ta karaya ba wajen ci gaba da wadannan ayyuka.

Wani tsohon dan tawaye, Malam Afar ya ce za su ci gaba da baiwa gwamnati hadin kai wajen gina kasa.