Jama'a na so a kafa kasar Palasdinawa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Palasdinawa, Mahmoud Abbas

Wani binkicen jin ra'ayoyin jama'a da BBC ta gudanar a kasashe goma sha tara, ya nuna cewa akasarin al'umar kasashen za su so ganin kasashen na su sun kada kuri'ar da za ta sanya Palasdinawa samun kasar kansu.

Hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da ake shirin fara taro a Majalisar Dinkin Duniya, inda ake sa ran shugabannin Palasdinawa za su bayyana bukatarsu ta samun kasar kansu.

Kamfanin jin ra'ayin jama'a na duniya maisuna Globsescan ne ya gudanar da binciken a madadin BBC.

Sakamakon binkicen ya nuna cewa kusan kashi arba'in da tara na duk mutanen da aka tuntuba, sun bayyana bukatar ganin kasashensu sun kada kuri'ar amince don baiwa Palasdinawa kasar kansu.

Kaso ashirin da daya na mutanen da aka tuntuba sun ce za su bukaci kasashensu su ki amince a baiwa Palasdinawa kasar kansu.