An kara kashe fararen hula a Yemen

An kara kashe fararen hula a Yemen
Image caption Mutane 26 aka kashe a ranar Litinin

An kara kashe fararen hula a zanga-zangar neman sauyin da ake yi a Sanaa babban birnin kasar Yemen, kwana guda bayan an kashe mutane 26 a birnin. Wadanda suka shaida lamarin sun ce jami'an tsaro sun bude wuta kan masu zanga-zanga, wadanda suka yi alkawarin ci gaba da yunkurinsu na kawar da shugaba Ali Abdullah Saleh.

Rahotanni sun ce akalla mutane ashirin aka kashe a tashin hankalin na baya-bayan nan.

Gwamnati ta musanta hannu a kisan na ranar Lahadi, tana zargin masu fafutukar Islama da bude wuta kan masu zanga-zangar.

Sai dai wadanda suka shaida lamarin da kuma masu zanga-zangar sun yi watsi da kalaman gwamnatin.

An shafe watanni dubban jama'a na fafutukar ganin karshen mulkin Mr Saleh, wanda a yanzu yake jinya a kasar Saudiyya sakamakon raunin da ya samu a watan Yuni.

Wani dan jarida mai zaman kansa a birnin Sanaa Tom Finn, ya rubuta a Twitter cewa jama'a da dama na zuwa wani asibitin wucin gadi, inda dama daga cikinsu ke dauke da harbin bindiga a kafafuwansu.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa cikin wadanda suka mutu a ranar Litinin har da wani karamin yaro da bashi da alaka da zanga-zangar.

Mahaifin yaron ya ce: "Na fita na bar yara na biyu a mota domin yin cefane, sai na ji babban yana ihu. An harbi karamin yaron a ka." Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar da rahoton barkewar fada a wasu sassan birnin, inda masu harbi a boye ke bude wuta kan masu zanga-zanga.

Karin bayani