AU ta amince da 'yan tawayen Libya

Hakkin mallakar hoto Getty

Tarayyar Afrika ta bayyana amincewarta da sabuwar gwamnatin wucin gadi ta 'yan tawayen Libya a matsayin gwamnati ta halali.

A baya dai Tarayyar Afrikar ba ta son amincewa da 'yan tawayen ba, kuma ta ma yi kokarin shiga tsakani don samar da zaman lafiya a kasar.

A cikin wata sanarwa, Tarayyar Afrika ta ce a shirye take ta goyi bayan yunkurin al'ummar Libya na samar da kasa mai hadin kai bisa tafarkin dimokuradiya.