IMF ya yi gargadi game da koma bayan tattalin arziki

Christine Lagarde,Shugabar hukumar IMF Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Christine Lagarde,Shugabar hukumar IMF

Asusun bada lamuni na duniya, IMF, ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar tattalin arzukin Amurka da na kasashen dake amfani da kudin euro na iya sake tabarbarewa, kuma muddin hakan ya faru, to zai lalata tattalin arzukin wasu kasashen.

Sabon hasashen da asusun IMF din ya ce tattalin arzukin duniya ya shiga wani halin kaka -ni-kayi.

Rahotan na IMF ya ce tilasne shugabannin kasashen Turai su yi aiki da matakan da suka amince da su a taron kolinsu da sukai a watan Yuli domin shawo kan matsalar.

Har ila yau rahotan na asusun IMF din ya ce tilas ne babban bankin kasashen Turai ya yi shirin rage kudaden ruwan da yake karba.