Za a raba abinci a Nijar

Image caption Mahamadou Issoufou

A Nijar, a yau Talata ne hadin gwiwar Hukumar Abinci ta Duniya tare da wata kungiya a Faransa ke shirin fara kai kayayyakin agaji ga iyalan da ke fama da matsalar karancin abinci a gundumar Mirriyah da ke jahar Damagaram.

Baya ga raba abincin dai za a baiwa wasu iyalan kudade kimanin dala miliyan dari biyu da za su tallafa musu wajen sayen abinci.

Wani jami'in Hukumar Abincin da ke Nijar ya ce mutane fiye da dubu hudu da dari biyar ne za su samu wannan tallafi.

Wadansu mutane da ke sa ran samun tallafin sun shaidawa BBC cewa suna bukatar tallafi game da yadda za su bunkasa noman rani, da kiwo don magance matsalar yunwar da suke fama da ita.