Kisan Rabbani: Karzai ya takaita ziyara

Shugaban Afghanistan Hamid Karzai, ya takaita ziyarar da ya ke yi a New York bayan da wani dan kunar-bakin-wake ya hallaka mutumin da ke kan gaba wajen sasanta gwamnatin kasar da kungiyar Taliban.

Dan kunar bakin waken ya hallaka Burhanuddin Rabbani ne a gidansa da ke Kabul, babban birnin kasar.

Tuni dai Shugaba Hamid Karzai ya bukaci jama'ar kasar da su ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya.

A yau Laraba ne kuma za a gudunar da taron gaggawa na majalisar zartarwar kasar don ganin yadda za a tunkari irin wadannan kashe-kashe.

Burhanuddin Rabbani, wanda tsohon shugaban kasar ta Afghanistan ne na ganawa ne da wasu 'yan kungiyar Taliban a lokacin da aka kashe shi.

'Yan sanda sun ce dan kunar bakin waken ya boye bam ne a cikin rawaninsa, inda ya tashe shi.