Masu fada-aji na kokawar neman iko a Yemen

Yemen Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun na samun goyon bayan masu fada a ji a kasar

Lokacin da guguwar sauyin da ke kadawa a kasashen Larabawa ta shiga Yemen a farkon bana, ta haifar da badakalar neman iko tsakanin bangarori uku.

Bangarorin sun hada da - iyalan shugaba Ali Abdullah Saleh, iyalan Ahmar da kuma babban jami'in soji Ali Mohsin - duka sun fito daga wasu gidaje na masu fada a ji a kasar.

Amma matsin lambar da makwannin da aka shafe ana zanga-zanga ta haifar tare da kuma hassada da suka nunawa juna, ya sa lamura sun tsaya cik.

A watan Maris, bayan da masu harbi daga nesa suka bude wuta kan masu zanga-zanga a birnin Sanaa, Janar Ali Mohsin ya raba gari da Mr Saleh.

Fada ya barke tsakanin iyalan Ahmar da kuma na Mr Saleh a gundumar Hasaba, lokacin da shugaban ya ki amincewa ya sanya hannu kan yarjejeniyar da kasashen Larabawa suka gabatar.

Fadan ya lafa bayan wani harin bom wanda ya jikkata shugaba Saleh.

Daga nan ne aka wuce da Mr Saleh zuwa Saudiyya domin jinya, kuma mataimakin shugaban kasa Abedrabbo Mansour Hadi ya ci gaba da jan ragamar mulki.

Sai dai har yanzu shugaba Saleh ya kasa cika alwashin da ya ci na dawowa Yemen.

Sabon tashin hankali

Al'amura sun kara rikicewa a farkon watan Satumba.

A ranar 12 ga watan satumba, Mr Saleh ya baiwa mataimakinsa ikon tattaunawa kan wani shiri na mika mulki.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Zanga-zanga ta barke a sassan kasar da dama

Kasashen duniya sun nuna kwarin gwiwa, inda gwamnatin Amurka ta ce tana sa ran kawo karshen matsalar cikin mako guda.

Amma masu adawa da shi sun nuna damuwa kan manufar shirin.

A ranar Lahadi, masu zanga-zanga sun yi kokarin kawo karshen takaddamar ta hanyar fita kan tituna domin zanga-zanga.

'Yan bindiga karkashin jagorancin magoya bayan Mr Saleh sun bude wuta kan masu zanga-zangar, inda suka kashe mutane 26.

Lamarin na ranar Lahadi ya haifar da martani daga bangaren Janar Ali Mohsin, wanda ya sha alwashin kare masu zanga-zangar da suka taru a dandalin sauyi.

An ci gaba da gwabza fada tsakanin magoya bayan Mr Saleh da kuma na Janar Ali Mohsin ranar Litinin a kusa da titin Zubayri da dandalin sauyi.

Akalla wasu mutanen 20 ne suka kara rasa rayukansu.

Rahotannin da ke fitowa a shafin musayar ra'ayi na Twitter na cewa dakarun Ali Mohsin na nufar fadar gwamnatin kasar ta Yemen. Fadan na ranar Litinin, na zuwa ne a lokacin da Hukumar Kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da yadda jami'an tsaron Mr Saleh suka yi amfani da karfi fiye da kima kan masu zanga-zangar.