Ana sa ran samun sakamakon zabe a Zambia

An samu barkewar rikici a kusa da rumfunan zabe da dama a Lusaka, babban birnin kasar Zambia, yayin da ake gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki da na kananan hukumoni.

A Wani wuri da ake kira Kanyama, wani gungun magoya bayan 'yan adawa sun hana a sauke takaddun zaben da suke zargin an riga an dangwale su.

Wakilin BBC ya ce bayannan kuma daruruwan matasa guje guje kan titi dauke da sanduna suna rewa wakar cewa sauyi suke so.

Matasan sun rika yaga hutunan shugaba Rupia Banda, mutumin dake fuskantar kalubale daga babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar Patriotic Front, wato Micheal Sata.