Yau ake gudanar da zabe a Zambia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Zambia, Rupiah Banda

A yau Talata ne za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan Majalisu a kasar Zambia da ke Afirka ta Tsakiya.

An tsaurara matakan tsaro a zaben, wanda masu sharhi suka bayyana cewa mai yiwuwa za a yi kan-kan-kan tsakanin 'yan takara.

Jam'iyar MMD ce ke mulkin kasar tsawon shekaru ashirin, inda shugaba mai-ci Rupiah Banda ya dare kan karagar mulki bayan mutuwar shugaba Levy Mwanawasa a shekarar 2008.

Duk da cewa kasar na samun bunkasar tattalin arziki sakamakon habakar cinikin ma'adanin copper, kashi biyu bisa uku na jama'arta na fama da talauci.