An kama makaman da aka yi safara a Anambra

Tutar Najeriya
Image caption Ana yawan kama masu fasakwaurin makamai a Najeriya

Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta kama wani mutum da ake zargi yana safarar makamai ba bisa ka'ida ba dauke da makaman.

Dubun mutumin da aka kaman ta cika ne a lokacin da 'yansanda suka kama wata babbar motar daukar kaya makare da alburusai da miyagun makamai.

Kuma rundunar tana ci gaba da gudanar da bincke kan lamarin.

Wannan kame dai ya zo ne dai-dai lokacin da Najeriya ke fama da rikice-rikice da ake dangantawa da kabilanci da addini, dai sauran matsalolin tsaro a Najeriyar.