An gano gawarwaki 35 a Mexico

Image caption Felipe Calderon na Mexico

Hukumomi a Mexico sun ce wasu 'yan bindiga sun watsar da gawarwakin mutune talatin da biyar a bayan wata motar a-kori-kura a tsakiyar wani babban kanti da ke jihar Veracruz ta gabashin kasar.

Rahotanni sun ce an daure hannayen wasu daga cikin gawarwakin, abin da ke nuna cewa an gallaza wa mutanen kafin a kashe su.

Jami'ai a yankin sun ce an gane mutane bakwai daga cikin gawarwakin wadanda ake zaton cewa suna da alaka ne kungiyoyin da ke aikata miyagun laifuffuka.

Jami'an sun yi amannar cewa an kashe mutanen ne sakamakon sa-in-sa tsakanin wasu kungiyoyi wadanda ba sa ga-maciji da juna.