An sabunta: 22 ga Satumba, 2011 - An wallafa a 13:41 GMT

An ci tarar wasu mata kan sanya Niqabi a Faransa

Niqab

Kenza Drider tana sanye da niqab a jirgin kasa

An ci tarar wasu mata biyu Musulmai a Faransa bayan da suka ci gaba da sanya Niqabi a bainar jama'a duk da cewa an haramta yin hakan.

An samu Hind Amas da Najate Nait Ali suna sanye da Niqabi a bainar jama'a a garin Meaux, da ke Gabashin birnin Paris, jim kadan bayan fara aiki da dokar a watan Mayu.

Matan sun ce za su daukaka kara kan hukuncin har zuwa kotun kare hakkin bil'adama ta Tarayyar Turai.

A bangare guda kuma, wata matar ta ce za ta tsaya takarar shugaban kasa da niqabin na ta.

Wakilin BBC a Paris Christian Fraser, ya ce ana sa ido kan hukuncin na ranar Alhamis ba wai kawai a Faransa ba, har ma a nahiyar Turai baki daya.

Belgium da Italy da Denmark da Austria da Netherlands da kuma Switzerland duka suna da irin wannan doka - ko kuma suna shirin kafa ta.

Idan ba a ci tarata ba ba zan samu damar daukaka kara ba. Dole sai an ci tarata tukunna sannan zan samu damar tafiya kotun kare hakkin bil'adama ta Tarayyar Turai

Hind Amas

Damar daukaka kara

Hind Amas, bazawara 'yar shekara 32, mai 'ya'ya uku, kotu ta ci tararta euro 120.

Kafin yanke hukuncin, ta ce tana so a ci tararta domin ta samu damar daukaka kara.

"Idan ba a ci tarata ba ba zan samu damar daukaka kara ba. Dole sai an ci tarata tukunna sannan zan samu damar tafiya kotun kare hakkin bil'adama ta Tarayyar Turai," a cewarta.

An kuma ci tarar Najate Nait Ali euro 80.

Sun zamo na farko da aka ci tara daga cikin mata 91 da 'yan sandan Faransa suka tare.

Amas ta shaida wa BBC cewa ta fara sanya niqab ne shekaru shida da suka wuce a matsayinta na budurwa mai ilimi.

Ta ce a baya tana sa siket ne iya cinya tare da zuwa wuraren sheke-aya, kafin daga bisani ta shiryu.

Wasu kungiyoyin Musulmi sun ce tun lokacin da aka sanya dokar, an ci zarafin mata Musulmai da dama a kasar ta Faransa.

Wata matar da ta yi suna wajen sanya niqab, Kenza Drider, ta ce za ta tsaya takarar shugaban kasar Faransa a shekara ta 2012.

Ta yi fice a cikin daruruwan matan kasar da suka dage kan cewa sanya niqabi ganin dama ne kuma dokar 'yancin dan adam ta Tarayyar Turai ta bayar da dama.

Ta bayyana cewa: "A zahiri akwai rashin aikin yi a Faransa, don haka kada mu yi la'akari da abinda na ke sanyawa, mu shawo kan babbar matsalar tukunna. Wannan shi ne abin da zan mayar da hankali a kai a takara ta."

Rabe-raben Niqabin da mata ke amfani da shi

 • Abaya
  Ana amfani da kalmar Hijab ne, wacce ta samo asali daga Larabci, domin siffanta Hijabin da mata ke sawa. Anahiyar Turai matan kan rufe kansu da jikinsu amma banda fuskokinsu.
 • Niqab
  Niqab kan rufe fuska sannan ya bar gurbin ido a bude. Sai dai akan yi amfani da shi tare da abin rufe ido na daban koma da dan kwali na musamman.
 • Niqabi Mai Raga
  Burka-wato Niqabi mai riga, itace mafi kyawun shiga ta musulunci, tana rufe baki dayan jiki da fuska, tare da barin kofa 'yar kadan.
 • Mayafi
  Shayla-wato Mayafi, yana da tsayi kuma ana amfani da shi sosai a kasashen Larabawa. Ana rataya shi tun daga kafada zuwa gadon baya.
 • Shari
  Chador-wato Shari, matan Iran ne suka fi amfani shi idan suna waje, yana rufe jiki gaba daya. A mafi yawan lokuta yana dauke da karamin mayafi.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.