Sufuri ya fuskanci tsaiko a Girka

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Shugaban Girka, George Papandreu

Bangaren sufuri a kasar Girka ya fuskanci tsaiko na sa'o'i ashirin da hudu, yayin da ma'aikata suka gudanar da zanga-zanga don nuna adawarsu ga matakan tsuke-bakin-aljihun da gwamnatin kasar ta bullo da su don magance matsalar basussukan da ke kanta.

Za a dakatar da zirga-zirgar motocin haya kuma ma'aikatan filayen jirgin sama ba za su yi aiki ba, inda kuma ma'aikata za su gudanar da zanga-zanga a tsakiyar birnin Athens.

A jiya ne dai gwamnatin kasar ta sanar da wasu sabbin matakai na samun goyon bayan hukumomin kasashen duniya da suke binta bashi.

Matakan sun hada da dakatar da ma'aikata dubu talatin, da kara rage kudaden fansho, da kuma kara yawan kudaden haraji.